Ranar Asabar 9/9/2017 ne za'a fafata a wasan mako na talatin da takwas 38 na gasar cin kofin Firimiya lig na tarayyar Najeriya, (NPFL) 2016/17 wanda kuma shine wasan karshe na shekara 2016/17 inda kungiyoyin kwallon kafa guda ashirin suka gwabza a tsakanin su,
A yanzu haka dai kungiyoyi biyu ne suka tabbata cewar sun Koma wasan kasa da firimiya, saboda rashin tabuka wani abun kirki kungiyoyin sune Remo Stars, sai Gombe United, daga jihar Gombe,
Haka kuma a wasan na goben za'a sake karkado wasu kungiyoyin guda biyu da zasu cika lisafin kungiyoyi hudu da za su buga wasan kasa da Firimiyar Najeriya.
kungiyoyi biyu kuwa ko waccenta tana fafutukar ganin ta lashe kofin ne a bana kungiyoyin sune Plateau United da take mataki na daya da maki 63 sai MFM FC, na garin Lagos, da take mataki na biyu da maki 62 kowaccensu tana da sauran wasa daya sai dai plateau united, zata kare wasanta a gida Ita kuwa MFM zata karkare wasantane a waje.
Ga kuma yadda jerin wasannin yake na ranar 9/9/2017
Plateau United, da Enugu Rangers,
El-kanemi da MFM Fc
Remo Stars da Sunshine,
.
Gombe United da Wikki Tourist
Ifeanyi Ubah da Lobi Stars,
Niger Tornadoes da Shooting Stars,
Akwa United da Kano Pillars,
Abia Warriors da Rivers United,
Enyimba da Kastina United,
Nasarawa United da ABS Fc,
Dukka wasannin za'a taka su ne da misalin karfe hudu na yammaci agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Facebook Forum