Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Kira ga Mutane da Suyi Hattara Wajen Anfani da Yanar Gizo


Yanar Gizo
Yanar Gizo

Amfani da kafafen yada zumunta na zamani ta yanar gizo wato social media Kamar yadda yake musamman a kasashen da suka ci gaba na taka rawar gani wajan tallata jam’iyun siyasa ko kuma ‘yan takara har ma da yin batanci ko cin zarafin wasu ‘yan takarar.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’azizu yayi hira da wasu mutane kamar su Mr Gynfan da kuma Malam Muhammadu Isma’il sun tofa albakacin bakin su inda suka yi bayanin cewar ‘yan siyasa na yin anfani da wadannnan kafafen yada labaru wajan nuna manufofin su kokuma yin batanci ga abokan hamayyar su.

Sun kuma kara da cewar yin anfani da kafar yada labarai ta yanar gizo kamar su Instagram, twitter, facebook, watsapp da sauran su na taka rawar gani kwarai musamman wajan yada guguwar canji a Nigeria, kuma hakan a cewar su, wata babbar nasara ce ga siyasar kasar da ma kasar baki daya. Saboda haka manyan kashen da suka cigaba ma da irin wannan kafafen suke anfani kuma sunyi tasiri kwarai.

Sai dai ganin yadda ake zargin anfani da wasu kafafen yada labarai wajan cin zarafin wasu ‘yan siyasa, kokuma ingiza mai kanto ruwa, babbar jam’iyar APC mai adawa a Najeriya ta bude gidan radiyon dan tallata hajar ta kuma har sun riga sun fara anfani da wannan gidan radiyo. a cewar shugaban kafafen yada labarai Alhai Umar Dan kane tura ce ta kai bango saboda rashin basu lokaci su tallata hajar su sai dai jam'iya mai mulki kawai.

##caption:Jam'iyar APC ta bude gidan rediyo.##

XS
SM
MD
LG