Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Yasa Auren Matan Fim Baya Karko


Mawakiya, kuma jarumar fina-finan Hausa, Sakna Gadaz
Mawakiya, kuma jarumar fina-finan Hausa, Sakna Gadaz

A satin daya wuce ne muka tambayi mutane cewa, ko Menene yake sa auren masu yin fina finai baya karko? Munyi wannan tambaya ne kasancewar idan aka duba yadda da zarar masu sana’ar fina finai sunyi aure ko a tsakanin ko a wajen wannan sana’a, mafi yawanci auren baya karko.

Mun sami amsoshi daga gurin masu sauraran mu da dama ga kadan da cikin amsoshin da muka samu. Hadiza Adamu, tace saboda sun saba da tafiye tafiye da kwana a otel dabam dabam, kuma su jarimai ne masu ji da kansu, kasancewar rayuwar aure bazata basu dama ta yawace yawace yadda suke so ba, ta kuma cigaba da cewa zaman aure na iya sanya musu iyaka wadda basu santa ba, mafi yawancin su kuma suna aurene badon soyayya ba sai don kudi ko suna.

Rabiya Balarabe tace, hardai ‘yan fim din yanzu da suke gani suna tare da manyan ‘yan siyasa, tunda irin su Halima Adam Yahaya suna can zaman su, ire iren ta wadanda basu dauki duniya da zafi ba Allah ya ganar dasu su san aure yafi komai daraja, in kaine yau ba kai ne gobe ba.

Auren sha’awa ne da kuma matan sun san namiji tun a titi, gashi idanun su ya bude basa jin kunyar komai, wannan ra’ayin Abudullahi Mohammed kenan. Ita kuma Badiyya Tijjani Babangida, cewa tayi basa yin aure a matsayin ibada ko soyayya kawai sun ‘dauki aure kamar kasuwanci.

Saurari sauran ra’ayoyin mutane game wannan tambaya.

XS
SM
MD
LG