Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayanin Malama Hadiza Balanti Kan Maza Masu Bata Matansu


Rashin sanin darajar ‘dan Adam shine ke haddasa wasu mazaje su rinka ‘bata matarsa ta gida alokacin da suke kokarin kara aure, da kuma tabbatar da ganin an rage mata daraja a idanuwan jama’a.

Hakan ne yasa muka nemi masaniya akan harkokin rayuwar mace da namiji, Malama Hadiza Balanti, inda tayi mana bayani cewa rashin sanin darajar dan adam na daya daga cikin irin wannan halayya, da kuma san zuciya. Namiji na ganin yin haka zai bashi dalili na kada a tambayeshi game da neman auren, musammam ma idan akwai abubuwan da ya kamata yayi ba karin aure ba.

Kasancewar aure ba’a neman izni wajen neman sa matukar an cika sharudan kara yin auren, yakamata maza masu irin wannan halayya suji tsoran Allah su guji wannan ‘dabi’a domin ba abune mai kyau ba, hakan ba dalili bane na inganci, hasali ma haramun ne kasancewar zagin musulmi fasikanci ne.

XS
SM
MD
LG