Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Su Guji ‘Daukar Doka A Hannun Su


Matasa suna kona tayoyi a zanga zangar kin jinin janye rangwamin man fetir.
Matasa suna kona tayoyi a zanga zangar kin jinin janye rangwamin man fetir.

A wata hira da Aminu Hassan Gamawa, ya shawarci matasa dasu rika bin doka da oda, wajen kawar da yanke hukunci ba bisa doka ba. Matsalar mutane su dauki doka a hannun su ko jami’an tsaro su yanke shukuncin nan take ba tare da gurfanar da mutum gaban kotu ba kamar yadda shari’a ta shimfida, matsala ce dake da girma kuma take maida kasa baya a harkar dimokaradiyya a ko’ina.

Harkar tsaro dai nauyi ne daya rataya akan gwamnati da jami’an tsaro, amma bazasu iya gudanar da wannan aikin ba har sai jama’a sun bayar da hadin kai. Kasancewar hare hare da ake kaiwa kan mutanen da basu ji ba basu gani ba, hakan ya sanya tsoro cikin zukatan mutane, inda da zarar ana zargin wani ko wata da cewar ‘yan kunar bakin wake ne to sai mutane su dauki mataki a hannun su, cikin rashin sanin gaskiyar lamari har a kashe mutum.

Babban kuskure ne yin hakan domin ka iya jawo ‘daukan rayukan wasu da basu jiba basu gani ba, hakan kuma na iya faruwa akan kowa, missali kashe wani shahararren farfesa na jami’ar Amadu Bello Zariya, bisa zarginsa da akayi masa cewa ko dan Boko Haram ne, hakan ta faru ne bisa ga rashin sani.

Hanyoyin kare hakan nada dama, jama’a nada kudunmawa da zasu iya taimakawa wajen kawo tsaro, na farko su saka ido wajen duk abin da ke faruwa a duk inda suke, da zarar sunga wani abu da basu yarda da shi ba su kira jami’an tsaro, haka jami’an tsaron suma suna da nauyin dake kansu na idan an sami wani da ake zarginsa da aikata laifi su bincike shi, idan an same shi da laifi a gurfanar da shi a gaban kotu domin yanke masa hukuncin da shari’a da tsarin dokar kasa ta tanada.

XS
SM
MD
LG