Ba ilimi ba ne ke kawo matsala tsakanin ma’aurata ba – inji mallam Hadi, shugaban sashin nazarin halayya da zamantakewar bil’ Adama na kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano.
Kamar yadda mallam Hadi yace, ba kowacce mace ce ba ke gane halayyar mijin ta ba idan ya dawo gida, kasancewar alokacin da mijin ke neman ta kafin ayi aure zai ta zuwa yana nuna mata soyayya da walwala, amma kasancewar anyi aure akwai abubuwa da dama da shi mijin zai iya haduwa na ‘bacin rai a gurin aiki ko a waje, hakan zai dawo dasu gida domin an zama ‘daya a wannan lokoci, to idan har macen bata san makamar da zata taryeshi ba, ko shi kanshi bai san yadda zai shigowa matarsa ba domin bai san irin halin da take ciki ba, hakan na kawo gushewar soyayya ga wasu ma’aurata.
Na miji dai kamar ‘dan siyasa yake, alokacin dayake neman a zabeshi kan wani mukami zai fadi kalamai mai kyau ga kowa da nuna kyawawan halaye, amma da zarar ya hau kujerar to sai a nemi wadannan halaye a rasa. To miji ma haka alokacin daya ke neman aure zai tafi hira cikin jin dadi da nuna soyayya, amma dazarar matar da shigo gida to fa mulkin sa zai fito fili, zai ji cewa gidan sa gidan mulkine idan yazo gidansa shi ya isa
Kuskuren da ake samu shine mace bata fuskantar wannan izzar, domin lokacin dayake zuwa zance gidan su kamar mai zuwa neman cin zabe ne, wani lokaci mazajen sun sani wani lokaci basu sani ba. Wannan hali na tasowa ne ga namiji alokacin da akayi aure, ya rinka ganin ai dole sai mace ta girmama shi. Ita kuma macen sai ta rinka ganin yaya mutumin nan da inyazo gidan su zai rinka wasa dariya da maganganun soyayya da dai sauransu, amma yanzu kuma zai rinka yi mata kunburi da nuna son shi wanine.
Rashin fuskantar hakan shine ke kawo karshen soyayya ga mace, ta rinka ganin mijin ya fiya girman kai da mugunta harma da rashin son ta kamar da, a takaice dai yama yaudare ta har tafara danasani ban aure shi ba. A daya bangaren kuma ita mace na son mijin ya cigaba da irin hirar daya ke mata alokacin da yake zuwa hira.
Saurari Mallam Hadi.