Domin kawar da shakka, kamfanonin wayoyin hannu sun kuduri aniyar cewa a bana idan Allah ya yarda, zasu sayar wa mutane agogunan hannu wadanda ke hade da wayar hannu ta salula.
An ga samfurin ire-iren wadannan agoguna da dama a kasuwa cikin wannan shekara ta 2015. Masu nazarin al’amurra sun ce kamfanoni su na kera wadannan agoguna da sauran kayayyakinsu cikin burge wa.
Ana kyautata tsammanin kamfanin Apple zai fitar da nasa a gogon hannun na farko a watan Afrilu, hakan zai sa wannan shekarar ta zamanto kan gaba wajen agogunan fasaha. Inji wata kungiyar bincike ta CCS a rahotanta.
Tsamanin da ake yi cewa za’a gabatar da irin wadannan agoguna, abokan gasar kamfanin Apple na nahiyar Asiya suna kokarin gabatar da nasu salon agogon a Barcelona ranar Lahadi mai zuwa, jajibirin ranar baje kolin na’urorin hannu daza’ayi nunin su a can Barcelonar.
Shima kamfani LG na Koriya ta Kudu, ya fitar da nasa agogon mai suna Urbane LTE, wanda shine kayataccen agogonsa na farko da za’a a iya kiran waya da kuma amsawa, batare da amfani da na’urar da ake sakawa a kunne domin magana ba.