Kamfanin Google, ya zuba jarin dala miliyan dari uku da saba’in da biyar, a kamfanin SolarCity domin samar da makamashin wutar lantarki ta amfani da hasken rana da zai rika baiwa gidaje dubu ashirin da biyar wutar lantarki.
Kamfanin makamashi na SolarCity, zai yi amfani da kudin ne wajen sa na’urorin samar da hasken rana akan gidaje, su kuma masu gidajen zasu rinka biyan wasu kudi duk wata na hayan wadannan na’urori daga kamfanin.
Jarin dala miliyan dari uku’n da Google ya zuba zai zamanto shine kudi mafi yawa da aka taba zubawa ga duk wani aiki na makamashi irin wannan.
A farkon watan nan ne kamfanin Apple, yace zai kashe dala miliyan dari takwas da arba’in da takwas kan makamashin amfani da hasken rana, domin gudanar da harkokinsa a California.
Wannan dai shine karo na biyu da kamfanin Google ya zuba jari a kamfanin SolarCity.
A shekara ta 2011, ne Google ya kafa wani asusun dala miliyan maitan da tamanin da mai kamfanin Tesla Motors Elon Musk ya marawa baya.
Hannun jari dai na kamfanin SolarCity ya hau da kadan, zuwa dala hamsin da biyu da kabo sittin da uku. Hannun jari kamfanin Google kuma, shima ya cira da wajen kashi biyu daga cikin dari.