Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa za su Kasa su Tsare su kuma Raka a Lokacin Zabe


Matasa sun tashi haikan wajen kara wayar da kan ‘yan uwansu da ma sauran jama’a, yayinda ake ta shirye shiryen babban zabe a Najeriya, na ranar 28 ga wata mai zuwa.

Malama Shema’u Ahmed Adam shugabar wata kungiya mai zaman kanta, ta fadi cewa ya zuwa yanzu dai matasa basu da wata damuwa, don ana samun cigaba. Matasa sun farga yanzu, ba za su yi siyasar kudi ba, ama zasu yi siyasar ‘yanci, su zabi wanda suke so wanda kuma suke gani zai zame masu alkhairi.

Malama Shema’u ta kuma ce In Allah Ya yarda zasu kasa, su tsare, su kuma raka lokacin zabe, kuma duk wanda yayi zabe tamkar yayi jihadi ne, tunda kayi ne don ka taimaka wa al’umma.

A karkashin kungiyar da shema’u ke jagoranta, ta ce suna cigaba da fadakar da mata akan yin rijista da kuma yin zabe.

“Duk da cewa ana fargabar zaben mai zuwa, In Allah ya yarda babu abinda zai faru saboda addu’o’in da ake yi” in ji malam Shema’u.

XS
SM
MD
LG