Rashin lafiyar mata masu juna biyu wani lamari ne mai hatsarin gaske, yana ma kuma karuwa a wannan zamani namu, daya daga cikin dalililan dake kawo hakan ya hada da rashin daukar kwararan matakan da suka kamata, kamar zuwa asibiti domin samun kula daga gurin kwararrun likitoci.
Hakan yasa wakilinmu ya tuntubi wasu magidanta domin jin ra’ayoyinsu game da maganar kai iyalansu asibiti musamman ma lokacin da suke dauke da juna biyu. Ya zanta wani magidanci mai suna Abubakar Sadiq, wanda ya bayyana cewa shi baya kai matarsa asibiti koda kuwa tana dauke da juna biyu, acewar sa bashi da wani amfani mutum ya dauki iyalansa ya kaisu asibiti, kasancewar da akwai iyaye mata da ungozomomi wanda zasu iya bada kulawa mai kyau ga matan masu juna biyu, yakuma nuna damuwar kan daukar matansu zuwa asibiti har wani kato ya gane masa mata, wannan abin damuwa ne a gurinsa.
A ra’ayin daya daga cikin mutanen da wakilin mu ya tattauna dasu, ya bayyana cewa baya kai matarsa asibiti dalilin sa kuwa shine indan za’a kai matan asibiti sai da kudi, yakuma ce idan babu kudi ko awo baza’a yi musu ba, kuma shi bashi da kudi.
Yawancin mutanen da suka bayyana mana ra’ayinsu kan rashin kai matan su asibiti musamman lokacin da suke dauke da juna biyu, shine suna bin al’adar iyaye da kakanni wajen amfani da ungozoma don karbar haihuwar ‘ya ‘yan su. Sai kuma dalilin su na biyu shine suna ganin bai kamata ba ace likita namiji zai duba musu mata domin yin hakan bai kamata ba acewar su.
Saurari tabakin mazajen.