Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayani Kan Yadda Matasa Zasu Nemi Ilimi – Dr. Aisha Abdu Isamail


wasu matasa na daukar jarabawa.
wasu matasa na daukar jarabawa.

Kwararriyar masaniyar harkokin siyasar nan ta Jami’ar Bayero, Dakta Aisha Abdu Isamail, ta yi bayanin yadda matasa za su nemi ilimi da tabbatar da wadanda aka zaba sun tsaya sun yi abun da ya dace.

Inda ta shawarci matasa da su samarwa da kansu kungiyoyi ga duk wasu abubuwa da suke kokarin cimma, hakan zai iya zamantowa ko a gurin aikine ko wajen sana’o’insu. Da kuma cigaba da neman ilimi da yin amfani dashi, da ilimantar da juna da yiwa juna nasiha.

A zamanin nan sai matasa sun san abubuwan daya kamata, wannan zai fara ne ta wajen girmama kansu, hakuri da yunwar yau domin tabbatar da gobe da jibi ga ‘ya ‘yan su harma da jikoki a gaba. Kaucewa san zuciya da abin duniya, kamar yadda ake amfani da kudi wajen sayen matasan ga karamin kudin da bai kai ya kawo ba har su aikata wasu abubuwan da zasu shafi al’umma da dama.

Daga karshe dai tayi kira ga matasa da subi nagaba da girmama su harma da daukar shawara, hakan nada matukar muhimmanci, kamar yadda ake cewa bin nagaba bin Allah.

Saurari Dr. Aisha Abdu Isamail.

XS
SM
MD
LG