Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa Kan Batun Ilimin Mata


A wani zaman mahawara da wakiliyar mu Madina Dauda ta jagoranta da wasu matasa a Abuja, sun tattauna ne akan ilimin mata, da yadda mutane ke ganin mata masu ilimi na gwada kansu dai dai dana mazajensu, ko kuma sun fi su.

Al-amin daya daga cikin matasan dake wannan zauren tattaunawar na ganin cewar babbar matsalar dake sanya wasu matan ganin cewar iliminsu wani mataki ne na rashin dai dai to ne tsakanin su da mazajensu, musamman idan sunfi su ilimi, wannan jin cewa ilimin wata daukaka ce a garesu, kuma hakan ba karamin jahilci bane, idan aka dube cewa darajar mace shine zaman auren ta, idan har ilimi zai sanya mata jin cewa tana da wata daukaka akan mijinta to har gwanda ta zauna da rashin ilimin.

Daya daga cikin matan dake wannan zaure Hajiya Safiya, ta nuna rashin amincewarta kan bayanan Al-amin, inda a ganin ta ilimin mace ya kasu kashi kashi, a kwai ilimin data samo daga gidan su wato tarbiyya, dakuma ilimin da ta samo daga makaranta, hada wadannan ilimi guda biyu ta yadda kowa zai karu dasu, to wannan shine ilimi na kwarai. Allah ya daurawa namiji nauyin kula da matasar kuma a karkashin sa take, amma yadda namiji ya shigo da tasa dabi’ar, wajen ganin mace nada ilimi da aikin yi, sai ya sakar mata da daukar nauyin gida wanda ya zamanto hakin sa ne, wannan shine ke kawowa mace taga cewa dai dai take da mijin ta.

Saurari cikakkiyar tattaunawar Madina Dauda da matasan.

XS
SM
MD
LG