Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wake Sana’ar sa Ido Maza ko Mata


Wasu mata suna dinkin hula a Agayawa jihar Katsina Nigeria.
Wasu mata suna dinkin hula a Agayawa jihar Katsina Nigeria.

Sa ido, a hausance na nufin shiga ko kula da lamarurrukan mutane da bai shafe ka ba. Wannan halayya na faruwa ga duk jinsuna biyu wato maza da mata, tambaya anan shin waye yafi Sa Ido a cikin jinsunan biyu?

Dakta Nu’uman Habib masanin halayyar ‘dan adam na jami’ar Bayero ta Kano, yace rashin adalci ne ace wai mata ne suka fi yin sa ido a wannan zamani namu, a kwai abinda mata sukafi sa ido akai, haka ma akwai abinda maza suka fi sa ido akai.

Idan aka duba sa idon mata za’a ga cewa idan mace ta shiga gidan buki, mata zasu kalleta kallon daga sama har kasa, daga suturar data saka har zuwa sarkokin ta da zoben ta, kuma ko nan da shekara daya aka tambayi daya daga cikin matan abinda matar ta saka na ranar to kuwa mata zasu iya tunawa, ba tare da sun manta ko mai ba. Amma idan hakan ta faru ga namiji, bayan kwana biyu ka tambayeshi wace riga wane yasa jiya ko shekaran jiya, bazai iya tunawa ba, sa ido dai kowa nayi sai dai ya banbanta tsakanin na mata dana maza.

Mutane na ganin cewar zaman banza ne ke kawo sana’ar sa ido, wani lokaci ana cewa sa ido sana’ar maras aiki, a tabakin dakta Nu’uman Habib, yace ba haka ake nufi ba, bawai mutane basu da sana’a bane, suna da sana’ar su harma suna da damar da zasu iya yin sa ido, abinda ake nufi kenan.

A wannan zamani duk inda aka samu wata sana’a mutane biyu uku nayi, suna kuma zaune a waje daya to cikin wannan zaman nasu da suke na wannan sana’a, idan dai bawani aikin karfi bane sukeyi, to sa ido zai iya shiga ciki, maganganun mutane da gulmace gulmace ba wai rashin aikin yi bane kawai ke kawo sa ido ba, a gurin aikin ma ana samu.

##caption:Wasu mata suna dinkin hula a Agayawa jihar Katsina Nigeria.##

XS
SM
MD
LG