Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashi Tamanin Cikin Dari na Masata ke Aure Bisa Sha’awa – inji Malama Hadiza Balanti


Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013.
Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013.

Rashin yin aure da manufa ingantacciya da rashin yin bincike akan auren tun kafin a ayi, hakika wadannnan abubuwa biyu sune mafarin rikici da fitintinu da zarar anyi aure.

A cewar malama Hadiza Balanti, kashi tamanin cikin dari na matasan yanzu sunayin aure ne domin biyan bukatun su na sha’awa, shiyasa aure baya samun nagarta da dadi irin na zamanin baya.

Idan aka duba zamanin baya lokacin da yara suke da tarbiyya, haka kuma iyaye ke kula da kaunar ‘ya ‘yan su za’a ga cewa ana samun yin aure har kala biyu, na farko shine na soyayya wanda saurayi da budurwa zasu gina soyayyar junansu har takai ga aure, na biyu shine auren da iyaye ke hadawa wato auren kyauta kona zumunci, inda iyaye zasu dauki ‘yar su subayar da ita ga duk wanda suka ga ya dace ita, hakan na iya zama a dangi ko a wajen iyali, kuma a zauna lafiya.

Abubuwa da dama ne ke kawo rabuwar aure a wannan zamani musammam ma a akasar hausa, da farko dai gina aure bisa makanta da karya sune manyan abubuwan da suke kawo rabuwar aure a wannan zamani namu. Wani lokaci kuma rashin hakuri da karbar kaddara na taka rawar gani wajen ruguza aure.

Komawa ga Allah, da tsayuwar tsayin daka ganin cewa kafin ayi aure anyi duk abubuwan da suka kamata na bincike da bin tsarin addini, batare da yin kwaskwarima ko dauki dai dai ba, da zarar anyi auren kuma abubuwa biyu ne ke tasiri da taimakawa wajen ganin an samu zaman lafiya, gaskiya da rikon amana dakuma hakuri da yarda da kaddara.

##caption:Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013.##

XS
SM
MD
LG