Hanyoyin sadarwa na yanar gizo na da matukar amfani a wannan zamani, kasancewar za’a iya amfani da ire-iren wadannan hanyoyi wajen koyarwa da ilimatar da mutane, hanyoyin dai sun hada da shafin facebook, Twitter, Instagram da dai sauransu.
Abdullahi Usman Maigaskiya, wani matashine da yake amfani da ilimin fasahar sa wajen hada da kafofin sadarwa na zamani ya bunkasa sana’ar sa ta daukan hoto.
Abdullahi na amfani hanyar sadarwa wajen tallata sana’ar sa ta daukar hoto, harma yana amfani da damarsa wajen nunawa mutane yadda yakamata ace ana daukar hoto, ya kuma bayyana yadda dabarun daukar hoto yake, ta yadda mutane bazasu kaucewa al’ada ba. Ya kuma bamu missalin yadda yake zuwa gidan buki irin na gargajiya domin daukar hotuna da kafe su a shafinsa na Instagram, wanda hakan ke sakawa mutanen da basu san al’adun Hausa sha’awa.
Shafinunan sadarwa sun zama makami mai karfi a wannan zamani, inda za’a iya amfini dasu wajen baza duk irin ilimin da akeso, duk da wasu matasan na ganin kamar abin wasa ne, ko yin amfani dashi wajen yada abubuwan da basu kamata ba.
Abdullahi yayi kira ga matasa masu kananan sana’o’i dasu yi amfani da ire-iren hanyoyin sadarwa wajen bunkasa sana’ar su. Matasa na iya amfani da hanyoyin sadarwa wajen daukaka duk wasu abubuwa da suke sha’awa ta inda zasu iya taimakawa kansu dama al’umma baki daya.
##caption:Shafunan sadarwa na zamani.##