Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Gargadi Gwamnatin Nijeriya


Wasu Matasa na tattauna makomar Nijeriya
Wasu Matasa na tattauna makomar Nijeriya

Wasu matasa a birnin Kano sun yi gangamin yin gargadi ga gwamnatin tarayyar Nijeriya na neman kar a sake dage zaben kasar kamar yadda su ka ce sun ji ana rade-radin yin hakan.

Daya daga cikin matasan mai suna Muhammad Sanusi Jibrin na kungiyar ‘Egalitarian Society of Nigeria” ya ce sun yi taron ne don su sanar da gwamnati da hukumar INEC da kuma duk masu shirin yin makarkashiyar tsai da zabe ko jinkirta zabe da cewa kar su yi hakan saboda su matasa za su yi zanga-zanga.

Matasan su ka ce muddun aka kasa gudanar da zaben ko kuma aka sake jinkirta shi, to hakan zai sa a nkasa iya kiyaye sauran dokokin kasa saboda shi ma zaben ya ginu ne bisa doka. Ya ce baya ga zanga-zangar ankarar da gwamnati da jama’a, akwai kuwa wasu matakan da za su iya daukawa. Ya ce har ma wasu na iya cewa bai kamata jami’an tsaron Nijeriya su tilasta wani ya bi doka ba tunda hukuma kanta ba ta bin dokar.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG