Domin nuna amincewa ga cigaban kamfanonin kera motoci na Najeriya, a jiya Lahadi ne shugaban kasa Gooluck Jonathan, yace nan ba da dadewa ba zai fara tuka motar da aka kera a Najeriya, kuma gwamnatin sa zata fara amfani da su a cikin ayarin motion shugaban kasa.
Wannan ya faru ne a wajen wani taro da wata kungiyar matasa mai suna “bada gudumawar ka” ta shirya, kuma anyi shine a otel din Eko dake Lagos.
Shugaban kasar dai ya kuma yi alkawarin tafiya da matasa cikin gwamnatin sa in har aka zabe shi a zabe mai zuwa, har ma yayi missali da tsohon shugaban kasa Janal Yakubu Gowon, wanda ya zama shugaban kasa a lokacin da yake da shekaru 33 a duniya, da tsohon gwamnan jihar River Diette Spiff, wanda ya zama gwamna kafin ya kai shekaru talatin a duniya.
A taron daya kunshi ‘dinbin matasan dake murna don samun damar haduwa da shugaban kasa, harma da yi masa tambayoyi cikin kwanciyar hankali.
Shugaba Jonathan dai ya basu tabbacin cewar lokaci lokaci zai rinka tattaunawa da matasa, domin ya samu damar jin ra’ayinsu, idan an zaben sa a kashi na biyu.