Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Sanda ya Harbe Shugabansa


Dan Sanda
Dan Sanda

Wani karamin dan Sanda ya harbe shugabansa mai mikamin Sufritandan ‘yan sanda, a jihar Bauchi, bayan da sukayi ‘yar takaddama.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda, na jihar Bauchi, DSP. Haruna Muhammad, wanda ya tabbatar wa wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, afkuwar lamarin, yace “Abunda ya faru shugaban ‘yan Sandan Mobile, na shiyar Bauchi, Sufritandan ‘yan Sanda Chris Eza, ya je rangadin ‘yan sanda, dake bakin aiki, akan hanya, sai ya tuhume dan sandan, domin rashin sa kayan sarkin a bisa doka sai ya bude mashi wuta.”

Ya kara da cewa a yanzu dai an kama shi wannan dan Sandan da yayi harbin sannan kuma Kwamishinan ‘yan Sanda ya bada umarnin a binciki wannan al’amari, saboda sanin dalilin yin wannan aika-aika.

XS
SM
MD
LG