Komawa tattalin arziki da ya dogara kan noma tilas ne ga tarayyar Najeriya, dalilin haka kuwa shine domin ana kara samun Nasara a nazarin samar da madadin man fetur ta hanyoyin daban-daban, kama daga makamashin rana, lantarki, tatsar mai daga Rogo, Rake ko Gansakuka.
Bugu da kari cikin ‘yan kwanakin nan an samu kasashe da dama wadanda suka samu man fetur a kasarsu, Amurka, wace ita ke kan gaba wajen shigar da man fetur tace nan da tsawon shekaru biyu zata wadata da man da take bukata. Wadannan alamu dai tafkar kadin kararrawa ne don farkawar Najeriya,
Duk da irin wadannan alamomi, Gwamnatin bata farka ba da sake lale zuwa ga noma, domin a da ya daga cikin tsofaffin Kwalejojin Fasaha da kimiyar noma dake arewacin Najeriya, a Jalingo, alamu a wannan makaranta yana nuni da cewa mahimman kayayyakin koyarda dalibai kamar motocin noma da dabbobin sun kaura daga makarantar.
Hugabar makarantar Dr. Elizabeth Wachap, tace duk da cewa Gwamnati jihar Taraba, na taimakawa makarantar, da kudaden gudanarwa, makarantar na iya komawa martabarta tada idan tana samun agaji daga asussun talafawa ilimi, na Gwanatin tarayyar Najeriya.
Jama’a, da daman a matukar mamakin yadda duk mai cikakken tunani zai byake Kwalejojin Fasaha da kimiyar noma daga asussun da ya farfado da mayarn makarantu da dama kuma ya taimakawa jami’an ta saun karo ilimi.