Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawa Da Kwararriyar Likitar Mata Dakta Mairo Mandara


mata da yara a asibiti.
mata da yara a asibiti.

Kula da lafiyar mata masu juna biyu nada matukar muhimmam ci, ga matan dakuma yaran da suke dauke dasu a cikin su. Sabanin yadda wasu magidanta ke ganin rashin amfanin daukar matan nasu zuwa asibiti domin a dubasu, sun dai gwammace da subi al’adar kaka da kakanni wajen barin matansu su haihu a gida karkashin kulawar ungozoma.

A dalilin hakane muka gayyaci masaniya a fannin ilimin lafiyar aure, da saduwar namiji da mata, kuma kwararriyar likitan mata Dakta Mairo Mandara, inda tayi mana bayani kan amfanin kai mata zuwa ganin likita, harma tace ba wai sai mace bata da lafiya kawai za’a iya kai ta asibiti ba, za’a iya zuwa domin neman karin lafiya da duba lafiya uwa da ‘dan dake cikin ta.

Data Mairo, tayi kira da a guji barin yaran da basu cika mutane ba su dauki ciki, domin wani abu ne babba kasancear in aka lura da yadda ake samun yawan mata masu samun cutar yoyon fitsari, kuma za’a ga cewar gajerun mata da yara kanana sunfi samun wannan cutar, hakan na faruwane dalilin rashin girman yaran.

Hanyoyin da mazaje zasu iya taimakawa wajen rage mace mace ga mata, musamman ma wadanda ke dauke da ciki ko suke hanyar haihuwa, Dakta Mairo dai tayi kira ga mazaje kan muhimmancin kula da matansu kamar kaisu asibiti da sayan magungunan da matan ke bukata, harma da samar musu abinci mai gina jiki da karin lafiya.

Yana kuma da mutukar amfani ga mata da zarar basu ga al’ada ba alokacin da suke da ciki, su rika zuwa asibiti akan lokaci domin a duba lafiyarsu.

XS
SM
MD
LG