Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Tambayi Yau da Gobe Tare Da Hadiza Balanti


Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013
Daurin Aure a Kano, Disamba 19, 2013

Kamar yadda wasu ke ganin cewa duk auren da aka biya sadaki mai yawa, to wannan auren fa baya albarka. Shugabar cibiyar bincike da wayar da kan mata tare da inganta lafiyar aure “Da Ke Ake” Hadiza Balanti Chediyar ‘yan Gurasa, ta musunta hakan alokacin da take amsa tambayoyin masu sauraro na shirin kutambayi Yau Da Gobe.

Hadiza Balanti dai tace wannan magana ba gaskiya bace, shi kuma sadaki bashi da iyaka ta sama amma yana da iyaka ta kasa, kamar yadda addinin musulunci ya tsara akwai adadin kudi da ya kamata a biya sadaki amma baza’a iya biyan kasa da wannan adadi ba, kuma Ko nawa mutum ya bayar sama da adadin nan to mutum baiyi laifi ba.

Sai kuma maganar yadda kayan lefe ke taimakawa wajen zamantakewar ma’aurata. Lefe dai na taimakawa ta fuskoki uku, na farko shine farantawa amarya, domin zatayi kwalliya ta kuma ji dadi kuma ango zai kalli amaryarsa yaji dadi, saukakawa kai shine fuska ta biyu domin zai rage wahalar zuwa sayo kayan kwalliya, kasancewar lokacin amarci shine lokacin da ma’aurata zasu zauna su hutu su kuma fuskanci juna har ma a tsara yadda yakamata rayuwa ta kasance a bisa tsarin addinin musulunci, fuska ta karshe zai zamanto kyautatawa ce ga amarya.

Sadaki dai sharadine babba a aure kuma wajibi sannan bashi da iyaka, Lefe al’adace daga cikin al’adun mallam bahaushe amma mai kyau, sadakin dai zai zamanto na mace ne amma Lefe zai zamanto na namiji ne.

XS
SM
MD
LG