Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa Da Madina Dauda


Taron Nunin Kaya Na Mata Musulmi A Abuja, Najeriya, Lahadai 27 Afrilu 2014.
Taron Nunin Kaya Na Mata Musulmi A Abuja, Najeriya, Lahadai 27 Afrilu 2014.

Acikin zauren tattaunawar mu na yau Madina Dauda, tare da wasu matasa sunyi muhawara ne game da yadda wasu mata ke kangarewa a makarantu duk da irin tarbiyar da iyayen su suka basu.

Duk abinda akayi batare da yin sa yadda yakamata ba to tabbas za’a samu miskila. A wannan zamani namu ana samun matsalar yadda ‘dalibai ke shiga wani hali, idan aka duba dalilan daya ya kai su makarantun. Makaranta dai ana zuwa ne domin neman ilimi, amma kasancewar wasu ‘daliban na koyar wasu ‘dabi’o’i da basu dace da ‘dabi’ar mallam bahaushe ba hakan na faruwa musamman ga ‘ya ‘ya mata ganin cewa suna koyi ga abinda wadansu matan keyi.

Ilimi da al’ada na tafiya tare idan aka duba cewa al’ada itace ke wassafa rayuwar mutane, missali ko a cikin addini za’a ga yadda wasu kyawawan al’adu suka kawata domin a tafi tare.

Saurari cikakkiyar muhawarar matasan.

XS
SM
MD
LG