Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Dan Iya Ya Kusa ‘Daukar Doka A Hannunsa


Wasu matasa kenan a kofar Majami'ar da aka kai wa hari
Wasu matasa kenan a kofar Majami'ar da aka kai wa hari

Dan Iya ya yanke shawarar ‘daukan doka a hannun sa, wajen yankewa kansa hukunci game da wasu abubuwa da suka dame shi a rayuwa, kicibis suka hadu da na Ikira.

Yau dai da ganin ‘Dan Iya, yace kai na Ikara zo kaji kar a barka a baya, daga yanzu fa duk wanda ya kawo mana wata hayaniya musammamma akan abubuwan da muka dauki aniya, to babu ko shakka zamu yi masa muguwar sakiya, idan ta kama ma mu hallakashi babu wani mai cemana mu tsaya, saboda mungano manyan mu sun mana tsiya tsiya, kasar mu komai na cigaba ya tsaya kuma idan ma muka je gurunsu don yin tambaya, sai suce mu dai muje mu ‘dauri juriya, idan mun juya baya mun barsu kuma suyi tayi mana dariya.

Sai ‘Dan Iya yace wannan nema dalilin da yasa mukace daga yanzu ba mu ba kara yin shiru, ayi ta cutar mu a kasa ace kuma wai muyi zuru musammam ma ganin yanzu rayuwa ta canza domin wayewa ma ta karu, kowanne matashi yasami sani tun daga farfaru, kaga ko koma mainene zai faru ya zama wajibi mu fara gwada kuru, da an tabamu kawai sai mu taru mu dunga daukar dokar duka don ta waru, ko da kuwa gwamnati zata yanke shawarar kiranmu tsageru, saboda suke sassakawa su dare kan manyan kujeru a karshe suyi mana tashin tartabaru.

Nace a a ‘Dan Iya, kada ku yanke shawarar daukar doka a hannunku, saboda koda kuwa wani ya yanke shawarar ya cuce ku to ya zama wajibi kubi dokar kasar ku, don itace tace idan wani yayi yunkurin lalata lamarinku to ku tuhumeshi gaban hukuma idan ya kama ma a kai shi ga kurkuku, da haka sai kaga an tunbuke duk wasu turaku, na masu yawon yada jita jita da futuntunu a tsakanin ku, saboda abin da duk arziki ya gaza baku to futuna da tashin hankali ma sam bai baku, don haka ‘Dan Iya, ku matasa kada ku kuskura wani ya kaiku ya baroku.

Dan Iya yace, Eh to na Ikara na amince zan tabbatar da na bijire wa duk kanin wasu rikice rikice, idan wani ya sassaka ya sadado min da jita jita zan tabbatar da na tantance zan kuma yi kokarin gujewa duk wani dandamali ko dandalin zaman cece kuce, idan aka jarraba jawoni cikin wata rigima ma zan kauce, kuma tun da ma fatan kowanne ‘dan kasa ya dace, daga yanzu zan yanke shawara na tabbatar da na jajirce in sami wata sana’ar da zan rike har sai na tabbatar da nayi fuce koda kuwa sana’ar dako ce ko yankan farce, saboda na tabbatar da sun fi tada futuna ko sace sace.

XS
SM
MD
LG