A cikin zaman mahawara da Murtala Faruk Sanyinna ya jagoranta da matasa, sun tattauna ne akan matsayin matasa mata da maza kan shiga harkokin shugabancin Najeriya, dama yadda matasan zasu saka ido domin tabbatar da cewa shugabanni dake mulki na yin ayyukan da sukayi alkawarin yi alokacin da suke naman kuri’ar ‘yan kasa.
Menene yakamata ace mata sunyi domin kawo ingancin shugabanci a Najeriya, musammam a yanzu da aka tunkari zabe? A ta bakin wata matashiya mai suna Ruth, tayi kira ne ga ‘yan uwanta mata da su sani cewar duk abin da zasuyi surika yin sane saboda gobe, ba dan yau kadai ba, tayi kuma kira ga matan da su tashi tsaye domin bayar da gudun mawarsu ga cigaban kasa.
Kasancewar matasa dai nada yawan gaske, to wacce hanyace matasan zasubi domin janyo hankulan shugabanni dama masu neman mukaman siyasa, ta yadda zasu kawo shugabanci na gari a Najeriya. Shikuma daya daga cikin matasan na ganin idan har an samu masata masu ilimi su fito suyi takara, yin hakan na iya kawo canji ga harkar shugaban ci a kasar, kuma irin canjin da ake nema zai faru ne idan har aka baiwa matasa damar samun ilimi.
Zaben shugabanni na gari shine zai zamanto mataki na farko ga samun cigaba, da kuma janyo hankulansu kan kula da bukatun jama’a, kamar tabbatar wa kan bunkasa ilimi ga matasa, Sukuma matasan su tashi tsaye domin nemawa kansu ilimi, domin ilimin nan idan bashi babu cigaban kasa.