Kwallon kafa a wannan zamani ta zamo wata hanya dake kara dankon zumunci ga matasa musamman ga Hausawa, idan aka duba yadda suke kallon wasan a cikin jama’a mai makon su kalli wasan a gidajen su daban daban.
A cikin wata tattaunawa da muharawa da wakilin mu yayi da wasu matasa masu sha’awar kallon wasan kwallon kafa kan sharshi da yadda wasannin ke gudana, na nunin cewa kallon wasannin kan kai matasan ga haduwa da sababbin abokai harma da kulla zumunci mai karfin gaske.
Wakilinmu ya duba yadda wasannin ke hada ire iren wannan zumuncin, wanda wasu lokutan ke haifar da taimakawa a tsakanin junan su, kamar yadda wasu matasan da wakilin namu ya samu zantawa dasu a wata cibiyar kallon wasanni suka bayyana masa. Alhaji Binji shine shugaban masu goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, yace “dayawa zamu zo kallon kwallo bamu san mutum ba amma saboda muna zama klub daya, daga nan zata kai ga musayar lambar waya, kana iya buga waya katambaya wane yaushe muke da wasa, to tanan dangantaka ta shiga idan kana da wata larura zaka iya bugo mishi wane ina da suna ko daurin aure, zakaga cikin jin dadi zai zo ya tayaka saboda dai wannan dangantakar da kuka samu a wajen kallon kwallo.”
Shima wani matashi mai suna Nura Shehu, ya shaida mana cewa da akwai mutane da dama daya hadu dasu a saboda kallon kwallo, har ta kai ga zumunta irin ta ‘daurin aure, suna da dai hidimomi daban daban, haka wani lokaci idan kazo gidan kallo sai kaga mutum ya dauki kudinsa ya biya maka kudin shiga.
Nasiru Mohammad Sani kuwa cewa yayi har kungiya suka hada ta magoya bayan kungiyar kwallon Real Madrid, wanda har tafiye tafiye suke zuwa wasu garuruwa domin haduwa da sauran ‘yan uwansu na sauran jihohi, hakan yasa har yanzu zumunci ya kulla zakanin su, duk lokacin da daya daga cikin zaiyi tafiya to zai nemi wasu daga cikin magoya bayan wasan idan suke karbar juna da karramawa da masauki da dai sauransu.
Ko shakka babu manazarta sunyi gaskiya inda suka bayyana ra’ayin cewa wasanni kan hada zumunci a tsakanin mutane wadanda suka fito daga gurare daban daban, ko suna wasan ne a tare ko suna kallo a tare, da kuma musammam tarayya a wajen goyon bayan kungiyar kwallo wanda a yanzu ya zama ruwan dare a Najeriya.