Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaima Ka Dara


A shirinmu na raha, yau mun sami labarin wani mutum ne da tafiya ta kama shi zuwa jihar Katsina da shi da wani abokinsa ana cikin tafiya an yi nisa kuma dama a cikin aljihunsa yana da naira dubu dari da hamsin.

Sa hannunsa a cikin aljihun sa ke da wuya sai ya ji an yi masa shafi mu lera, ba kudi ba kamarsu, zunbur ya mike tsaye ya ce wa mai mota ya tsaya an wawushe shi kuma dole a tsaya a caje kowa idan ba haka ba abinda ya faru a shekara ta 1998 zai maimaita kansa.

Ko da jin haka fasinjoji suka firgita ko me ya faru? ku biyo mu domin jin abinda ya faru a shekara ta 1998 …

Saurari cikakken shirin a nan..Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG