Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Samsung Da Apple Zasu Koma Kotu


Apple Samsung
Apple Samsung

Kamfanin Samsung ya ‘daukaka kara a kotun kolin Amurka, kan hukuncin laifin kwafar fasaha da aka yanke masa a baya, a shari’ar da aka dade ana gwabzawa tsakanin sa da kamfanin Apple, kamar yadda takardun kotun suka nuna.

Shigar da takardun dai yazo ne bayan da kotun daukaka kara ta amince da wani bangare na hukuncin da karamar kotu ta yanke, ta kuma umarci Samsung da ya biya zunzurutun kudu har dala miliyan 930 kwatankwacin Naira miliyan dari biyu, ga kamfanin Apple.

Makon daya gabata ne dai wasu takardun kotu ke nunin cewa ‘daukaka karan zai maida hankali kan yadda zanen fasahar yake, da kuma asarar da satar fasahar ta janyo.

A baya bayan nan ne dai kamfanin Samsung ya sami nasara bayan da aka bada izinin sake lissafa asarar da ya janyo wa takwaransa Apple, amma masu wakiltar kamfanonin sun bukaci a dakatar da komai har sai anga yadda kotun koli tayi.

Sake lissafin zai iya shafar wani bangare na kudin da kotu ta bada izinin a baiwa kamfanin na Apple har kimanin dalar miliyan 382, kan laifin kwafar fasaha da kamfanin mai tushe a Koriya ta Kudu yayi na kwafar siffar sabuwar wayar nan ta Iphone ta kamfanin Amurka wato Apple.

Kamfanonin fasaha da dama na cikin irin wannan dambarwar inda ake shigar da kara a fadin duniya, wanda wasu kamfanoni ke zargin takwarorin su da laifin sace musu fasaha ba tare da izini ba. Amma dai wannan danbarwa tsakanin Apple da Samsung ta janyo hankalin mutane da dama kasancewar sune manyan kamfanonin wayar hannu biyu a duniya da kasuwar fasaha.

XS
SM
MD
LG