Babban Alkali a wata Kotun Amurka dake cikin jihar Minnesota, ya bada umurnin a tasa keyar wani dan kasar Bosnia, wanda ya kantara karya akan rawar da ya taka a laifin yaki, sa'ilin da ya yi gudun hijira zuwa nan Amurka a shekarar 1998.
Zdenko Jakisa dake zaune a tsibirin dake kusa da wani gandu a babban birnin jihar Minnesota, yana cikin kungiyar nan data yi kaurin suna wajen kisan 'yan Croatia a lokacin yakin da aka yi a kasar a shekarar 1990.
Shi dai wannan dan talikin an yanke masa hukuncin aikata ayyukan ashsha, ciki kuwa har da kashe wata dattijiyar Serbia bayan ya dirka mata bindiga daga tagar ta lokacin tana cikin dakin ta, kuma ko baya ga wannan yana da wasu hukunce-hukuncen ayyukan ashsha a kansa amma ya gudo yazo nan Amurka kuma ya shara karya lokacin shigowar sa kasar.