Kasar China ta kirkiri na’urar kwamfuta da ta fi kowacce saurin sarrafa bayanai a duniya wato Supercomputer a turance, a cewar wani jerin sunayen kwamfutocin da suka fi sauri a duniya.
Ita dai wannan kwamfuta da kasar China ta kirkira mai suna TaihuLight itace tazo ta farko a jerin sunayen, tana amfani da manhajar Linux, haka kuma zata iya yin lissafi kala kala har Tiriliyon Dubu 93 cikin dakika ‘daya. Wanda hakan ya ninka saurin sarrafa bayanan da kwamfutar da ta zo ta farko a shekarar da ta gabata sauri.
Idan aka duba cikin shekaru goma da suka gabata China na da Supercomputer har 28 a jerin sunaye da ake da su 500, cikinsu kuwa babu wadda tazo matsayi na 30 a jerin sunayen, sai gashi kasar ta shiga gaban kowacce kasa a fagen sarrafa supercomputer.
Yanzu haka dai China na da Supercomputer 167 cikin jerin 500 masu sauri, kuma ta wuce Amurka wadda ke da 165.
Baki daya duk na’urorin da akayi amfani da su wajen kera wannan kwamfuta kuwa an kirkiresu a China, wanda ya kawo karshen maganar da akeyi na cewa dole sai China ta dogara da kasashen Turai kafin a dama da ita a fannin wannan fasahar.
China dai zatayi amfani da wannan kwamfuta a fannoni da dama da suka hada da aikin injiniya mai zurfi da ayyukan kirkira da kuma nazarin sauyin yanayi.