Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa na Manchester United, dan kasar Belgium, Marouane Fellaini, mai shekaru 29, da haihuwa tana iya yuwar bazai samu damar fafatawa a wasan da kungiyarsa ta Manchester zatayi tsakaninta da takwararta ta Liverpool, ba ranar Asabar 14/10/2017 a gasar Firimiya lig, wasan mako na takwas, sakamakon raunin da yasamu.
Shidai dan wasan ya samu raunin ne a wasan da kasarsa ta Belgium, tayi tsakainta da kasar Bosnia, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 2018 da za'ayi a kasar Rasha.
Ranar Asabar da ta gabata 7/10/2017, ne kasar Belgium tabi Bosnia, har gida ta doke ta da kwallaye 4-3, Fellani ya samu raunin ne a cikin minti na 29, da fara wasan.
A wani labarin da kasarsa ta Belgium, ta wallafa a shafinta na yanar gizo mai yuwar dan wasan zai iya shafe sati biyu yana jinyar kafarsa don haka Fellaini, bazai samu damar fafata a wasan da Kasar Belgium zatayi da kasar Cyprus, ba a ranar Talata 10/10/2017 a cigaba da fafutukar neman gurbin cin kofin kwallon kafa na duniya.
Facebook Forum