Kunngiyar masu horar da ‘yan wasa na kananun kungiyoyin kwallon kafa dake jihar Bauchi, a tarayyar Najeriya, (Grafca) tayi bikin murnar chika shekaru Goma da kafuwar.
An dai kafa wannan kungiyarce a shekara ta 2007, farkon sunan kungiyar YOFCA wato Youth Football Coaches Association Of Bauchi, daga bisani ta Koma GRAFCA, Grassroot football Coaches Association Of Bauchi, a shekara 2016.
An kirkiro wannan kungiyarce domin tallafawa kananun kungiyoyin wasan kwallon kafa da kuma zakulo da ‘yan wasan na cikin gida.
Shuwagabanin kungiyar sunyi jerin gwano sanye da riguna mai dauke da tambarin kungiyar ta Grafca, tare da ‘yan wasa yayin nuna farin cikinsu bias irin nasarori da kungiyar ta samu da kuma irin gudumawar da suke samu daga gwamnati da kuma hukumar kula da kwallon kafa ta (FA) na jihar Bauchi tare da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa.
A yanzu haka kungiyar na da rajista kungiyoyin kwallon kafa 190, da matasan masu wasan kwallon kafa fiye da dubu biyar, tare da kungiyoyi ashirin, wadanda suka jagoranci kungiyar sune Coach Kasimu Bello (Okey) da Komerit Ahmad Sale Bununu, (Jibros).
Facebook Forum