Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ce tafi yawan yara da basa makaranta - MDD


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da fatan zai mika sabbin dokoki ga majalisa kan dakile lalata da yara mata da hukunci mai tsanani kan fyade
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da fatan zai mika sabbin dokoki ga majalisa kan dakile lalata da yara mata da hukunci mai tsanani kan fyade

Haruna Muhammad Babale na ganin hanyar da za'a bi a cike gibin dake akwai tsakanin matalauta da masu arziki a Najeriya ita ce ta ilimantar da jama'a saboda yanzu Najeriya ce tafi yawan yara da basa makaranta kamar yadda alkalumman Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice suka nnuna

Dole sai an ilimantar da mutane a tarbiyantar dasu da samar masu da hanyoyin samun aikin yi domin rage radadin talauci.

Haruna Muhammad Babale ya kira 'yan siyasa da manyan masu kudi su ji tsoron Allah. Idan kana da kudi yau kana anfani dashi ka dauki yar wani ka kaita Dubai ka yi lalata da ita to gobe Allah na iya mayar da kai matsiyaci. A sani akwai mutuwa kuma duk abunda mutum ya aikata sai Allah ya tambayeshi.

Yace ya kamata gwamnati ta shigo lamarin amma abun tambaya shi ne wace irin gwamnati kuma su wanene cikin gwamnatin. Su wanene zasu iya daukan matakin da za'a tabbatar dashi a kuma yi abun da ya dace. Saidai idan jami'an gwamnati da yakamata su aiwatar da dokar su ne suke karyata to babu abun da za'a iya yi.

Akwai mafita. Alumma ce zata tashi ta tilastawa gwamnati sai tayi wani abu. Amma al'umma ba zata yi hakan ba sai an wayar da kanta.

Dokokin da ake anfani dasu yanzu tsoffi ne. Yakamata a yi wasu da zasu yi tasiri. Haruna yace a dauki fyade a matsayin misali hukuncin da ake yi bai taka kara ya karya ba. Hukuncin ba zai sa masu yin fyade su ji tsoro ba.

Ga cikakken bayani

XS
SM
MD
LG