Yayinda yake jajantawa 'yan kasuwar Kano da suka yi hasarar dukiyoyinsu a gobarar kasuwar Sabongarin Kano Sarki Sanusi II ya gargadesu cewa bayan addu'a kamata ya yi su binciki kansu dangane da rayuwarsu a matsayin masu tsoron Allah.
Mai ba gwamnan Bauchi shawara akan harkokin labarai Kwamred Sabo Muhammad ya kara haske akan irin kokarin da gwamnatin ke yi domin warware matsalar ilimi a jihar
A firar da ya yi da Muryar Amurka a nan Washington DC gwamnan Bauchi Barrister M. A. Abubakar ya bayyana yada zai yi anfani da tallafin kudi na miliyan 58 daga Amurka domin inganta harkokin ilimi a jihar
Masana a jami'ar Bayero dake Kano Farfasa Kamilu Sani Fagge da Dr Abba Fagge sun zanta da muryar Amurka akan taron nukiliya da kuma ita nukiliyar kanta
Shugaban Najeriya tare da tawagarsa suna cikin wadanda suke cikin taron nukiliya da ake yi yanzu a Washington DC fadar gwamnatin Amurka
Ilimi a jihar Bauchi ya tabarbare inda hatta kujerun da yara zasu zauna su dauki karatu babu a kusan duk makarantun jihar haka ma akwai malamai da suka yi shekaru da dama ba'a kara masu girma ba kuma su kan yi wata da watanni ba'a biyasu albashi ba.
Haruna Muhammad Babale na ganin hanyar da za'a bi a cike gibin dake akwai tsakanin matalauta da masu arziki a Najeriya ita ce ta ilimantar da jama'a saboda yanzu Najeriya ce tafi yawan yara da basa makaranta kamar yadda alkalumman Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice suka nnuna
A muhawarar da aka yi da iyaye mata da maza sun bayyana dalilan dake sa masu kudi da masu iko ke lalata 'ya'ya mata
Lokacin da dalibai ke daukan jarabawar share faggen shiga jami'a da suka yi da komfuta sun samu matsala da naurar wadda ta dinga mutuwa