Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwar Fulani a Amurka


Dubun dubatan mutane a kasashen Afrika na da tunanin cewar a kasashen Afrika ne kawai ake da Fulani ko nace makiyaya. To ba abun mamaki bane, a kasar Amurka akwai turawa Fulani, wadanda suke gudanar da rayuwarsu kamar ta Fulani da aka fi sani a kasashen Afrika, wato rayuwa a cikin daji dagasu sai dabbobinsu. Suma wadannan Turawan Fulani suna kiwon dabbobin su kamar yadda Fulani Afrika keyi, sukan yi tafiye tafiye daga wani guri zuwa wani guri sukan kuma yadda zango a wurare daban da ban kamar yadda Fulani kanyi a kashaen afrika. Kuma wani abun ban mamaki shine sukanyi noma a duk inda suka samu kansu don gudanar da rayuwa mai’inganci.

Babban muhimin abu a nan shine, na samu ziyartar rigar wasu turawa Fulani a jihar Fensilbeniya, wadda muka tattauna da wani makiyayi me suna Mr. Lyode Anyat, wanda yayi mun Karin haske dangane da ilimin ‘yayansu. Yace ‘yayansu na zuwa makaranta a kowace rana a kowane irin yanayi, na sanyi ko na zafi, wanda daga bisani idan suka dawo gida sai su tafi kiwo ko suje gona, yace kiwo baya hana ‘yayansu karatu. Ya kuma yimun Karin haske kancewar idan akwai bukatar su kara gaba, daga inda suke to duk garin da suka isa, su kan sa ‘yayansu makaranta kamin su matsa gaba don dai kada abar ‘yayan nasu a baya. Yace sukan bar wuri zuwa wani zango akalla ba’akassara ba sau biyu ko uku a shekara.

Na kuma yi tattaki zuwa wata makarantar ‘yayan makiyaya duk a cikin jihar ta fensilbeniya, wadda nayi katar da shugaban makarantar Malama. Kate Bacha, tayi mun Karin haske dangane da kulawar da suke ba ‘yayan makiyaya kamar yada ake bawa kowane yaro, babu banbanci. Tace sukan karbi yara akowane irin lokaci iyayen yara suka iso garin su, don basu damar da yakamata. Tace a wasu lokutta idan iyayane wadannan yaran suna da bukatar matsawa zuwa gaba idan yayi dai dai da lokacin jarabawa sukan ba iyayen shawar su dan dakata sai yaran sun gama zangon karatun, kana sukan bama yaran takardar shaida yadda idan suka isa wani gari sai su nuna don cigaban karatun su. Na kuma tambayeta wai shin gwamnati na ba wadannan yaran kulawa kuwa?

Sai tace, ai wadannan yaran basu da banbanci da sauran yara, hasalima cikin wadannan yaran akansamu masu hazaka fiye da yaran da suke a cikin gari, don gwamnati na iya kokarinta wajen samar da wadatatun kayan karatu da nagartatun malamai a wadannan makarantun, ka ko ga kuwa ashe yaran ma zaka taraddasu da maida hankali. Sai na kara tambayar, wai shin menene matakin karatu na malami ko malama zasu sama kamin su fara koyar da yara?

Sai tace ai dokace anan babu wanda zai koyar da yara sai yana da karancin digirin jami’a ko sama, kuma sai ya samu takardar shedar koyarwa kamin su barshi ya shiga aji ya koyar.

Wannan na nuni da cewar akwai bukatar gwamnatoci a kasashen mu na Afrika su tashi tsaye wajen inganta ilimin ‘yayan makiyaya a ko ina. Suma iyaye makiyaya yakamata su sani cewar wannan ilimin na zamani na da matukar mahimanci idan suka bar yayan su suka same shi akowane irin hali suke ciki. Su tabbatar da sun tura yayansu makaranta kamin wani abu a kowace rana, don ta haka ne kawai za’a iya samun cigaban kasa. Muhimin abu anan shine, iyaye Fulani su sani cewar ilmantar da ‘yayansu shine kawai hanyar cigaban kasa, kasncewar Fulani sun kushi kaso mafi yawa a kasashen mu na Afrika musamman a Najeriya.

Jama’a masu sauraro, muna masu kara kira da babbar murya da iyaye makiyaya su sa ‘yayansu makarantu don cigaban tattalin arzikin kasa, ana kuma kira ga wadanna da su kaji wannan kiran da su taimaka su isar da shi ga wadanda basuji ba, don ta haka ne kawai zamu samu wayewar kai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG