Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojan Nigeria tace Rade-Raden da ake yi na kafa gwamnatin wucin gadi a Nigeria basu da tushe


Rundunar sojan Nigeria ta baiyana zarge zargen da ake yi cewa hafsan sojojin Nigeria, yana shirye shiryen jan ragamar gwamnatin rikon kwarya, idan har jam’iyar masu hamaiya ta lashe zaben shugaban kasar da za’a yi.

A wata sanarwa, mai magana da yawun sojojin Najeriya, Col Sani Usman yace, sojoji sun ‘dauki wannan labari a matsayin abu mai hatsarin gaske, kuma bashi da wani tushe, idan aka yi la’akari da irin sadaukar da ran da sojoji suka yi domin goyon bayan dimokaradiyya.

Yace, ba za’a yarda da wannan yunkuri da ake yi da gangan domin dakushe yarda ko kuma amincewar da jama’a suka nunawa sojoji ba.

Mai magana da yawun sojin Najeriya, Col Sani ya cigaba da cewa, “sojojin Najeriya basu da wani ra’ayi a siyasa kuma bazasu jurewa duk wani shugaban soja ko soja daya tsoma kansa cikin harkokin siyasa ba.”

Yace, Sojojin Najeriya suna lura da kuma mutunta ka’idodin tsarin mulkin kasar.

Ya kamalla da yin gargadi ga ‘yan siyasa da wakilansu ko kuma yan koren su, da su guji yunkurin cusa soja cikin harkokin siyasa.

XS
SM
MD
LG