Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Wasannin Da Aka Buga Na Premier League


Sakamakon wasan da aka buga na premier league na kasar Ingila na shekarar 2016/2017 mako na biyar tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da Liverpool a filin wasa na Stamford Bridge, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Chelsea da ci 2 -1 a gidan Chelsea

Dan wasan Liverpool mai suna Dejan Lovren, shine ya jefa kwallo ta farko a ragar Chelsea, cikin minti goma sha bakwai da fara wasa.

Liverpool ta sake samun nasarar jefa kwallonta ta biyu ta kafar dan wasanta Jordan Henderson, a yayin da ake minti talatin da shida kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ita kuwa Chelsea ta samu damar jefa tata kwallonne a yayin da ake minti sitin da daya na wasan daga dan wasanta mai suna Diego Costa.

Wannan dalilin ya ba kungiuyar Liverpool damar komawa mataki na 6 a teburin premier league, da maki 1 a maimakon na 6 da take da farko.

Ita kuma kungiyar Chelsea ta sauko daga mataki na 2, ne zuwa mataki na 5 a teburin gasar premier league.

Ranar Asabar 17/9/2016

Man City 4-0 AFC Bournemouth.

Leicester City 3-0 Burnley.

Hull city 1-4 Arsenal.

West Bromwich 4-2 Westham.

Ita ma Everton ta samu nasara 4-2 akan MiddleBrough

A jiya lahadi Kuwa, kungiyar kwallon kafa ta Watford ta samu nasara akan Man Utd da ci 3-1.

Crystal Palace Ta lallasa Stoke city ne daci 4-1

Southampton 1-0 Swansea city.

Itama Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta sha Sunderland 1-0.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG