Sanata Ahmed Lawan, mai wakiltar mazabar Yobe, ta Arewa a majalisar dattawan najeriya ya bukaci shugaba Goodluck Jonathan, da ya bayyanawa ‘yan kasar sabbin matakan da gwamnati ke dauka domin dakile ayyukan ‘yan kungiyar Boko Haram a kasar.
Sanatan ya bukaci hakane a yayin wata ganawa da yayi da ‘yan jaridu a Kano, ya koka ainin kan tabarbarewar tsaro a yankin arewacin Najeriya, musamman arewa maso gabashin kasar.
Ata bakin Sanatan yace, “ abinda ya faru a Damaturu ranar Litinin sai wanda ya gani, kuma abinda ya faru a Kano Juma’a sai wanda ya gani, dole ne shugaban kasa ya fito yayiwa mutanen kasarnan bayani kan me ake ciki na sabon tsarin daya yakamata yayi na kare ‘yan Najeriya.”
Ya kara kira ga shugaban kasar Najeriya da yayi koyi ga shugaban kasar Kenya kan duk wanda bai yi aikin sa daidai ba to a koreshi daga aiki, kasan cewar mutane 35 da aka kashe a Kenya saida shugaban kasar ya kori ministan sa na cikin gida, har shugaban ‘yan sandar saida yayi murabus don ganin za’a koreshi.
Sanatan ya kara da cewa muddin shugaban kasar yaki yin hakan, su kuma a matsayinsu na wakilan jama’a basu da zabi illa su dauki matakin daya dace a kansa.
Saurari tabakin Sanatan