Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sepp Blatter Na Kokarin Canza Ra'ayin Sa


Shugaban hukumar kwallon kafa ta FIFA Sepp Blatter yace bazai sauka daga kan kujerar sa kamar yadda ya yi alkawari da farko cewar idan Allah ya kaimu watan biyu na shekara mai zuwa, zai sauka daga kujerar tasa a sakamakon zargin sa da hukumar binciken Swiss Investigators ta yi da yin almubazaranci da dukiyar hukumar.

An zargi Hukumar binciken da rattaba hannu akan wata kwangilar da bata yi ma hukumar ta fifa dadai ba, wato kin yin biyayya wajan biyan wasu kkudade ga Shugaban UEFA Michel Platini.

Blatter ya fito karara ya fadi cewa bashi da wani laifi kuma bai aikata wani abu da yake ba bisa doka ko ka’ida ba.

Shima Platini ya rubuta wa mambobin kungiyar UEFA wasika ya kuma musunta zargin.

A wani jawabin da shugaba Blatter ya rubuta wanda lauyan sa ya gabatar, ya ce adadin fan miliyan 1.5 da aka biya shugaban UEFA Platini a shekarar 2011 ba wani abu bane wanda ya wuce diyyar da aka biya kungiyar.

A halin da ake ciki dai duka shugabannin biyu na fuskantar bincike daga hukumar ta FIFA.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG