An sake mika ma dan shekaru 53 nan wanda ya taba jagorantar tawagar ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya a watan Nuwambar shekara 2013 wato Stephen Keshi, jan ragamar tawagar.
A shekarar da ta gabata ne yayin da Najeriyar tayi nasarar kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya a kasar Brazil kwangilar da aka bashi ta kare. A lokacin da yaja ragamar kungiyar da farko, Keshi ya lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a sheka ta 2013.
“Kwamitin kungiyar kwallon kafa ta kasa ya zauna a ranar larabar da ta gabata kuma ta kai karshe wajan sa hannun cimma yarjejeniyar mayar da Keshi domin cigaba da zama kocin kasar” a cewar Pinnick.
“Munyi imanin da ya cancanci ci gaba da jan ragamar tawagar ‘yan wasan kuma muna sa ran zai sa hannun a kan sabuwar yarjejeniyar a kwana kwanan nan”
Kuma ana bukatar Keshin zai sa hannu akan yarjejeniyra girmama ka’idojin da’a da sanin yakamata, ya kuma yi tafiya da hukumar kwallon kafar ta Najeriya.