Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sun yi Garkuwa da Sakatarorin Ma'aikatar Kananan Hukumomin Biyu


Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu
Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu

Tsofaffin kansiloli a jihar Neja, sun gudanar da wata zanga-zangar neman biyan su wasu kudade da suka ce suna bin Gwamnatin Jihar.

Zanga-zangar dai da aka yi a harabar ma'aikatar kananan hukumomin jihar ta kusa zama tarzoma domin kuwa har kansilolin sun share yini jiya suna tsare da wasu wasu sakatarorin kananan hukumomin a wani dakin taro dake ma'aikatar.

Yahaya Shehu, shugaban kungiyar tsofaffin kansilolin yace sun yi garkuwa da sakatarorin ma'aikatar kananan hukumomin su biyu ne domin basu gamsu da bayani da suka yi masu ba yana mai cewa sun zo ne su bi hakkinsu wadda yakamata a biyarsu wata uku da kama aiki gashi yanzu watan su takwas da barin aiki har yanzu ba'a biya su ba.

Ya kara da cewa kowane daga cikinsu kansilolin 274 yana bin Gwamnatin jihar Neja miliyan uku da dubu da dari biyar.

Sakataren Gwamnati jihar Ailhaji Idris Ndako yace babu abunda za'a iya yi yanzu domin idan har za'a biya albashi to tabbaci hakika nasu kudaden bazasu samu ba.

XS
SM
MD
LG