Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarar Dala Dubu Biyar Da CAF Ta Ci Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya


Jiya tsohon ministan matasa da wasanni na Najeriya Col Musa Mohammed mai ritaya ya kwatanta tarar da hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta ci hukumar kwallon kafa ta Najeriya na kudi dala dubu biyar a sakamakon barin 'yan kallon da suka fi karfin adadin da filin wasa na Ahmadu Bello stadium ya kamata ya dauka a lokacin da kungiyar Super Eagles ta kara da kungiyar kwallon kafa ta misira a matsayin mai sassaucin gaske.

Tsohon ministan wanda ya nuna bukatar 'yan wasan Super Eagles su rika buga duk wani wasa da zasu yi a filin wasan Abuja a hirar sa da mujallar Daily Trust jiya, ya bayyana cewa tarar dala dubu biyar ta yi kadan a irin wannan lamarin da ya faru.

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Afirka ta sawa hukumar kwallon kafa ta Najeriya tarar kudi dala dubu biyar ne a sakamakon barin jama'ar da yawan su yafi karfin yadda aka tsara domin 'yan kallo a filin wasan Ahmadu Bello Stadium dake jahar Kaduna

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG