Wasu mutane bakwai sun gami da ajalinsu sakamakon tashin wani bom a tsakiyar kasuwar Biu, dake kudancin Borno a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Wannan tashin bom din yazone a dai dai lokacin da hukumar zabe ta dage zaben kasar, bisa dalilan inganta matakan tsaro musammam ma wanda ke addabar shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Shedun gani da ido sun shaidawa Muyar Amurka, cewa bom din ya tashine da missalin karfe uku na rana, kuma a ranar da ake cin kasuwar wannna gari a kusa da wata sabuwar kofar shiga kasuwar wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwan, da kuma jikkata wasu ashirin da shida.
Wannan abu dai yasa matasan garin kara kaimi na cigaba da bincikar ababan hawa, da kuma daukar kwararen matakan tsaro. Ko a watan jiya ma an samu wasu ‘yan bindiga sukayi kokari shiga garin, amma rundunar soja da matasan garin suka taka musu birki, inda aka halaka yawancin maharani.
Lamarin dai yasa mutane dama jimami da firgita musammam ma ‘yan kasuwar kasancewar wannan hari shine na farko da aka samu tashin bom a cikin kasuwa ta garin Biu.
Shugaban riko na karamar hukumar Biu Alhaji Umar Kadafur ya tabbatar wa da wakilinmu afkuwar lamarin, ya daice mutane bakwai sun rasa rayukan su.
A yanzu haka dai an sami daidai tuwar lamura a cikin garin Biu, sai dai cigaba da bincikar ababan hawa da kuma kara kaimi da matasan keyi na ganin irin hakan bai kara faruwa ba.
Saurari rahotan Haruna Dauda Biu.