Kungiyar Boko Haram daga Najeriya ta kaddamar sabbin hare hare a Nijar da kamaru jiya litininin, a dai dai lokacin da shugaban kungiyar yayi alwashin galaba kan sojojin kasashe da suke fafatawa dasu.
Shaidun gani da ido suka ce 'yan bindiga sun kai hari kan wani gidan fursina a kudu maso gabasshin Nijar a garin Diffa, amma sojojin Nijar suka kore su. Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan yawan mutane da harin ya rutsa dasu, ko akwai kuma fursinoni da suka tsere.
Daga bisani aka samu rahotani da arewacin kamaru cewa, mayakan sakan sun kama wata motar Bas da mutane akalla 18. Wani mazaunin wani gari da ake kira Koza ya gayawa kamfanin dillancin labaran Associted Press cewa mayakan sun tuka motar zuwa ta kan iyakar Najeriya.
A wani fefen bidiyo da aka saka a dandalin Youtube, ya nuna shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau yana ba'a ga rundunar sojojin yanki dubu bakwai da ake shirin girkewa, cewa ai sunyi kadan, domin mayakansa zasu karkashesu daya bayan daya.
Haka nan kuma yayi barazana ga shugaban Cadi Idris Deby, wanda sojojin kasarsa suka fafata da mayakan Boko Haram a Najeriya da Nijar da kuma kamaru cikin makon jiya.