Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wanene Dan Takarar Majalisar Dattijan Borno Ta Tsakiya, Sanata Ali Modu Sharif Ko Kwamarad Baba Kacalla?


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Da alamu akwai wata sabuwar rigima dake kokarin kunno kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Borno, kan wanda zai kasance mata dan takarar majalisar dattawa a Borno ta tsakiya.

Bangaren tsohuwar jam’iyyar PDP dai ta gabatar da kwamarad Baba Kacalla, yayin da bangaren tsohon gwamnan jihar Borno sanata Ali Modu Sharif, ke cewa tsohon gwamnan ne dan takarar ta, wannan batu dai ya dade ana ta ja in ja tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyun wadda har ta kai ga daya daga cikin ‘yan takarar kwamarad Mohammed Baba Kacalla, shaida wa manema labarai cewa wannan kujerar takarar a hannun sa ta ke, kuma koda a yanzu haka hukumar zabe mai zaman kanta shi ta sani ba tsohon gwamnan ba kamar yadda yake ikirarin cewa shine dan takarar kujerar majalisar PDP na Borno ta tsakiya.

Tsohon gwamnan jihar Borno sanata Ali Modu Sharif, ya dai fice daga fice ne daga jam’iyyar APC zuwa PDP wadda sakamakon rashin jituwa da suka samu tsakaninsu da gwamnan jihar Borno hon Kashim Shattima, wanda tsohon kwamishinan sa ne alokacin da yake gwamna, tun shigarsa zuwa PDP dai wasu magoya bayansa suke bayyana cewa tsohon gwamnan ne zai yi musu takara a matsayin ‘dan majalisa mai wakiltar Borno ta tsakiya. Wanda a baya ya bayyana wa manema labarai cewa, magoya bayansa sun saya masa fom din takara amma yana nan yana shawara kan tsayawar ko rashin tsayawar sa.

Wakilin mu Haruna Dauda, ya tuntubi shugaban jam’iyyar PDP na jihar Borno Alhaji Baba Basharu ta wayar tarho, wanda ya shaida masa su sunan kwamarad Baba Kacalla, ne suka bada kuma shine hukumar zabe mai zaman kanta ta karba a matsayin dan takarar majalisar dattawan Borno ta tsakiya.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Direct link

XS
SM
MD
LG