A yayin da ake cigaba da maida martani a game da babban zabe a Najeriya, wanda yanzu haka ma masana harkar tsaro a kasar suka bukaci shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, da su hanzarta yin murabus sakamakon matakin da suka dauka na cewa bazasu iya tabbatar da tsaro ba a kasar lokacin babban zabe.
Dalilin da yasa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayarda sanarwar dagewar zaben, dakta Bawa Abdullahi Wasai, wani masanin harkar tsaro akasar, yace sojojin Najeriya sun baiwa kasar Najeriya kunya a idon duniya, inda ya cigaba da cewa, “An siyasantar da aikin soja, an siyasantar da kwamandojin askarawan soja dalilin da kenan ake amfani da bakin jama’a a ci musu albasa, idan kuma a bisa dalilin da suka bayar idan a kasa ne wadda a kwai shuwagabannin na masu gaskiya, da a ranar Asabar din nan da jami’an tsaro suka fito suka ce bazasu iya kare wani abu da ya shafi zabe ba to da yakamata ace duk sunyi murabus, ko kuma a sallamesu.”
To sai dai wasu ‘yan Najeriya sun ma danganta wannan matsayi ne da jami’an tsaron suka dauka da juyin mulki ga tsarin dimokaradiyya, batun da sukace bazai razana su ba.
A yanzu dai an zuba ido ne aga yadda matakan jam’iyyu da kuma ‘yan takara dama sauran kungiyoyin sakai zasu dauka, inda a bangare guda kuma wasu suke barazanar zuwa kotu.
A yanzu haka dai jami’an tsaro ne ke cikin shirin ko ta kwana ke cigaba da shawagi a manyan biranan kasar.
Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’Aziz.