“Ko bayan bama nan Najeriya zata cigaba da wanzuwa, dan haka ya zama dole magoya baya su maida zuciya nesa.” Inji Janar Buhari a taron maida martani kan dage babban zaben Najeriya, da tsawon makonni shida.
Buhari dai yace, ya zama wajibi sabuwar ranar zaben ta zama tamkar zanen dutse, don jam’iyyar sa bazata lamunci cigaba da shishshigin al’amarin hukumar zabe ba. Ya cigaba da cewa, “mu abinda muka sa a gaban mu shine zama lafiya da wadatar al’umma, kuma tunda abin nan da su hukumar zabe sukayi sunyi shi cikin ka’idojin mulkin Najeriya, ba abinda zamuyi illa muyi hakuri wadannan ranaku suzo, amma mun gaya musu a cikin kudun mulkin Najeriya wannan shine dabara ta karshe da zasuyi, wadannan ranaku bazasu iya canja su ba, amma munce zamubi hanyar dimokaradiyya ta kundin mulkin Najeriya, zamu jajirce ayi zaben nan ran ashirin da takwas ga watan uku da ran sha daya ga watan hudu. Idan kuma gwamnati ta gaza yi to sai dai ta baiwa sojoji mulki ko kuma tace ta kwace mulki babu ruwanta da dimokaradiyya, su kuma ‘yan Najeriya su suka san yadda zasuyi da su.”
Shi kuma sakataren kwamitin amintattun jam’iyyar PDP, sanata Walid Jibrin, ya musanta wannan makarkashiyar dage zaben. Inda yace, “PDP ba ita bace, kawai don tana mulki sai tace a canza wannan zabe, to ta canza saboda me takeso a canza. ya kuma yi kira ga shugabannin adawa da su rinka baiwa mutanen su hakuri, su tsaya su ga karshen wannan abun kada wani ya fito yayi tashin hankali, kada ayi kone kone, kada a farfasawa mutane motocinsu, hakan shine zai kawo zaman lafiya yasa wannan zargi da ake yiwa PDP ya zama bayyananne.”
Kungiyoyin fararen hula dai na cigaba da zanga-zangar neman wanzuwar mulkin dimokaradiyya a Najeriya, a yayin da guguwar fitina ke tinkarar nasarar mulkin.
Saurari cikakken rahotan Nasuru Adamu Elhikaya.