WASHINGTON, DC —
Kamfanin Transcorp Nigeria PLC yana kokarin samo kudi har dala miliyan dubu daya domin gina tasoshin samar da wutar lantarki a Najeriya. Babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Obinna Ufudo yace yana jin nan da watan Janairun 2015 zasu hada hancin kudaden domin gina tashar da zata samar da megawatt dubu 1 na wutar lantarki.
Kamfanin Transcorp na daga cikin wadanda aka sayarwa da hannayen jarin kamfanonin wuta a Najeriya, inda ya sayi tashar samar da wuta ta Ughelli a Niger Delta.
Haka kuma, kamfanin Transcorp yana da masana’antar sarrafa ‘ya’yan itatuwa a jihar Binuwai.
Bayan wadannan, kamfanin Transcorp yana harkar hotel inda yake shirin gina wasu guda uku kan kudi dala miliyan 500 a Abuja da Lavgos da kuma Jihar Rivers. Sannan yana shirin inganta hotel dinsa mai suna Transcorp Hilton a Abuja.