Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Twitter Za Tayi Gyara A Shafinta


FILE - The Twitter logo is shown at its corporate headquarters in San Francisco, California, April 28, 2015.
FILE - The Twitter logo is shown at its corporate headquarters in San Francisco, California, April 28, 2015.

Kamfanin shafin sada zumuncin Twitter zai cire Makala hoto a shafinsa a matsayin lissafin kalmomi 140 da aka kaiyade rubutawa a shafin, saboda haka hoto zai zama mai zaman kansa sannan kalmomi 140 da aka saba suma suyi zaman kansu.

Wannan kafa dai na samun tsaiko wajen kara bunkasa da samun karin mutane. A watan da ya gabata ne shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey, yace kamfanin zai yi gyara a wani yunkurin janyo hankalin mutane zuwa Twitter.

Ya ci gaba da cewa kamfanin na ganin akwai damar yin gyara ga wasu kofofi da ke kawo tsaiko wajen ci gaban kamfanin.

Yanzu haka dai duk lokacin da mutum ya kafe adireshin shafin yanar gizo da yake so mutane su shiga, adireshin na daukar kimanin kalmomi 23 zuwa sama daga cikin kalmomin da aka kaiyade amfani da su 140.

Twitter dai na samun tsaiko wajen bunkasa, haka kuma hannun jarin kamfanin yayi kasa da kaso 70 a shekarar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG