Shirin samartaka na wannana makon ya sami zanatawa da matasa daban daban daga sassan Najeriya domin jin ra'ayoyin su akan irin rawar da iyaye maza da mata ke takawa wajan taya 'ya'yan su maza da mata zabar abokan aure na gari domin samun kyakkyawar makoma.
Dashike ba'a taba taruwa aka zama daya ba, kowa da irin nasa ra'ayin musamman ma ganin yadda zamani ya canza kuma kamar yadda masu iya magan suka ce, idan kida ya canza, rawa ma canzawa take.
Daya daga cikin matasan ya bayyana ra'ayinsa cewar abin da yafi dacewa shine tunda zamani ya canza, yakamata iyaye su bar 'ya'yan su su dogara da kansu domin nemo wa kawunan su abokan soyayyar gaskiya domin kuwa so da kauna shine zaman aure.
Wasu daga ciki sun ce hakan bai dace ba domin kuwa a cewar su, abin da babba ya hango yaro ko ya taka turmi bazai gani ba. Dalilin cewa hakan kuwa shine idan soyayya ta shiga zuciyar mutum babu yadda za'a yi yaga aibu, ko laifin abokin soyayyar sa dan haka wajibi ne iyaye su bincika domin samarwa da 'ya'yan su abokan zama na gari
Ga cikakkiyar hirar.