Shahararren ‘dan wasan kungiyar Chelsea Didier Drogba ya bayyana cewa wasan su na yau Lahadi da kungiyar Sunderland shine zai zamanto wasansa na karshe a Chelsea.
Ya dai fitar da sanarwar ne ta cewa wasan nasu na ‘karshen kakar bana da Sunderland, shine wasan sa na karshe da Chelsea, saboda yana son zuwa ya gwada bugawa wasu kungiyoyin.
Drogba dai ya taimakawa Chelsea wajen zama zakaran wasanni da dama ya kuma jefa wa kungiyar kwallon daga kai sai gola a wasan gasar Champion League na karshe da kungiyar Bayern Munich wanda suka lashe gasar ta shekara ta 2012.
Ata bakin ‘dan wasan Drogba ya bayyanawa shafin yanar gizon kungiyar Chelsea dalilin sa na yanke hukuncin barin kungiyar Chelsea in da yace, “Ina son na ‘kara buga wasa a kalla kakar wasa ‘daya, hanyar da zanbi domin na cigaba da buga wasan kwallo shine na tafi wata kungiyar. Duk magoya bayan kungiyar sun san son da nake yiwa kungiyar Chelsea, kuma ina fatan dawowa kungiyar a wani matsayi nan gaba.”
Tun shekara ta 2004 Drogba yazo kungiyar Chelsea kuma yaci kwallaye 157 a bayyana wasanni 341, ya kuma samu damar zakaran wasan Champion League har sau uku.